Hakan dai ya bada dama wajen cimma yarjejeniyar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta Cimawa na kokarin ganin an samu kawo karshen yakin da suka dauki tsahon shekaru suna tafkawa da juna a arewacin kasar. Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Malin Mongi Hamdi ne ya bayyana hakan inda ya ce daya daga cikin matakan yarjejeniyar ya bukaci da a tsagaita wuta a garin Menaka da ke arewacin kasar da kuma janyewar mayakan sa kai da ke goyon bayan gwamnatin ta Mali a yankin, inda ya ce za a maye gurbinsu da dakarun Majalisar Dinkin Duniya zuwa wani lokaci. Su dai 'yan tawayen Malin na fafutukar samar da 'yancin kan yankin Abzinawa ne wanda suka yiwa lakabi da Azawad.ABNA
6 Yuni 2015 - 10:45
Lambar labari: 693981
Hukumomi a kasar Mali da 'yan tawayen Abzinawan kasar sun ratafa hannu kan wata yarjejeniya da ta bukaci a tsagaita wuta a tsakaninsu.